Daga Ahmed Ilallah
A ranar 27/8/1991 gwamnatin soja karkashin shugaba General Badamasi Babangida ta kirkiri Jahar Jigawa da wasu jahohin, wanda a yanzu Jahar ta cika shekaru 34 da kirkira.
Shin a wannan lokacin da Jahar take da shekaru 34, a wane ma’auni za a nuna girman tattalin arzikin Jahar.
Shi tattalin arziki jaha shine ginshikin cigaban wannan Jahar, shine zai taimakawa gwamnati wajen samun kudaden da za a yiwa kasa aiki.
Tabbas, banda kudaden da jahohi suke samu da tarayya, samun kudaden shiga daga gida zai taimakawa gwamnati wajen sauke nauyin da ke kanta.
Samun irin wannan kudade yana samuwa ne, yayi da tattalin arziki jaha ya bunkasa.
A yau jahohin da suke da cigaba, za ka iske wannan jahohi sun sami bunkasar tattalin arzikin su ne.
A tsawan shekaru 34 na Jihar Jigawa har yanzu jahar ta dogara kwachankwaf ne a kan kudaden da a ke rabawa na tarayya. Kudaden da a ke samarwa na cikin gida bai taka kara ya karya ba.
Ko a wannan lokacin da a ke ganin wannan kudaden ya karu, kudaden bai kai 6% na kasafin kudin Jahar ba.
Ana iya samun irin wannan kudaden kawai in har tattalin arzikin yana kara girma.
Kusan za a iya cewa bunkasar tattalin arzikin Jahar Jigawa ya kasance Kalubale da duk gwamnonin da suka shugabancin wannan Jahar.
Duk da kasancewa ita jahar Jigawa jaha ce ta karkara, wanda kusan duk yankunan ta karkace, garuruwan da za a iya ce musu birane kadan ne.
Amma duk da haka Jahar Jigawa tana da arziki na noman rani da damina, tana damar kasuwanci na tsakanin kasa da kasa.
Amma rashin kyakkyawan tsari na gina tsarin tattalin mai dorewa don bunkasa tattalin arzikin Jahar.
Gwamnonin wannan Jahar sun fi maida hankaline wajen kawata Jahar da aiyukan da basu da tasiri akan bunkasa tattalin arzikin Jahar.
alhajilallah@gmail.com








