Daga Ahmed Illallah
Samar da sabuwar dokar Haraji da Gwamnatin Tinubu tayi yana daga cikin muhimman kuduri da aiki da wannan Gwamnatin ta cimma, wanda ya gagari shugabannin baya.
Wannan doka tun farkon aiyana ta wannan kudiri na doka ya sha suka, adawa, zargi da kuma rashin daidaito da fahimta a tsakanin, masu ruwa da tsaki, yan majalissa, gwamnoni, talakawan kasa da bangaren Gwamnatin Tarayyar.
Bayan kai ruwa rana, Gwamnatin ta samu daidaito na wani bangare na dokar tsakanin ta gwamnaoni, musamman wajen rabon harajin VAT da wasu bangarorin.
Hakazalika a Majalissas Dokoki ma an samu yanayin wannan kalubalen, kafin suyi gyararrakin su, su kuma aiwatar da dokar.
Tsugunne bata kare ba a kan wannan doka ta Haraji duk da sanya mata hannu da Shugaba Tinubu yayi
Tun lokacin da Gwamnatin Tinubu ta aiyana soma amfani da dokar a watan January 2026, kusan za a ce hayaniya da hauragiya ta kacane a kan wannan doka.
Baban abun damulawar ma shine, hatta wasu yan majalissa Dokoki na zargin cewa dokar da a kayi mata Gazette don aiwatar wa ta saba da kudurin dokar da amince da ita.
Baban abun damuwa a kan batun wannan doka shine har yanzu Yan Nijeriya basu ma fahimci dokar ba, da kuma yadda biyan harajin ma zai kasance.








